
Majalisar dattawa a ranar Laraba, ta gayyaci Sifeton ‘yana sanda na kasa IbrahimK. Idris domin ya bayyana a gabanta ya bayyana mata yadda aka yi ‘yan sanda suka ci zarafin Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, DIno Melaye.
Haka kuma, Sifeton ‘yan sandan zai amsa tambayoyi game da yadda ake cigaba da kai hare hare a jihohin Binuwai da Taraba da kuma Zamfara.
Jaridar DAILY NIGERAIN ta ruwaito cewar,’yan majalisar dattawan karkashin jagorancin Shugaban majalisar Bukola Saraki, sun jingine cigaba da tattaunawa a yau domin zuwa asibitin da aka kwantar da Dino Melaye su duba lafiyarsa.
Sanata Melaye ya jiwa kansa ciwo ne a lokacin da ya diro daga motar ‘yan sandan da take dauke da shi akan hanyar su ta zuwa Lakwaja domin gurfanar da shi a can.
Da sanyin safiyar Laraba, ‘yan sanda sun hana wasu sanatoci guda hudu ganin Dino Melaye, sanatocin sun je asibitin ne karkashin jagorancin Bala Ibn Na’Allah domin ganin halin da Melaye yake ciki a asibiti.
Sai dai kuma, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood ya bayyana cewar Sanata Melaye ya sulale daga tarkon ‘yan sanda tun a ranar Talata.
“Da misalin 1200 ne Sanata Dino Melaye da yake bayan kanta a ofishin ‘yan sanda, a yayin da ake yunkurin kaishi babbar kotun tarayya dake Lakwaja daga Abuja, ya tsere daga inda ake tsare da shi a bayan kanta bisa taimakon wasu ‘yan daba, da suka zo da motoci guda biyu, suka tarewa motar ‘yan sanda hanyar dake dauke da Sanatan a Shataletalen Arewa 1, a wannan lokaci ne Sanatan yayi alkafura inda ya nemi ya fada motar da ‘yan daban suka zo, inda daga bisani kuma mutanen suka gudu da Dino Melaye wani wajen da ‘yan sanda basu sani ba”
“Daga bisani ‘yan sanda suka sake bibiya har suka gano Sanata Dino Melaye yana asibitin Zankli dake birnin tarayya Abuja,inda aka kuma kama shi a asibitin. Rundunar ‘yan sanda zata kuma gurfanarda Dino Melaye a kotu ba tare da wani bata lokaci ba”
“Haka kuma, ‘yan sanda sun ci nasarar kkama motar da wasu ‘yan daba suka yi amfani da ita domin kubutar da Dino Melaye daga hannun ‘yan sanda”
“Sai dai kuma tuni, Sifeton ‘yan sanda na kasa ya bayar da umarnin gudanar da binciken yadda aka yi Sana Dino Melaye ya gudu daga motar ‘yan sanda da kuma yadda aka sake kamo shi bayan ya gudu” A cewar Jimoh Moshood kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa.