
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta bayyana cewar ta fara shirin yiwa dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma kiranye, domin ta fara duba sa hannun al’ummar mazabarsa da zai bada damar dawo da Dino daga wakilci a majalisar dattawa.
Sanata Melaye yanzu haka yana karbar magani a babban asibitin kasa dake Abuja, sakamakon raunin da ya samu bayan da ya fado daga motar da ‘yan sanda ke dauke dashi zuwa Lakwaja domin fuskantar tuhuma.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta habarto cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta,INEC, ta sanya ranar 28 ga watan Afrilu domin fara shirin dawo da shi gida. Da yake bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Lakwaja, babban kwamishina a hukumar Mohammed Haruna, yace zasu fara shirin ddawo da dan majalisar kamar yadda doka ta tanada.
Ya bayyana cewar zasu fara gudanar da atisayen dawo da dan majalisar ne a akwatuna 552 a yankin kananan hukumomi bakwai dake yankin mazabar dan majalisar dattawa ta jihar Kogi ta Yamma.
A cewarsa, atisayen za’a fara shi ne da misalin karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana, ta hanyar amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’ah, domin tantance mutanan da suka sanya hannu a takardun dawo da Melaye gida.
“Wadan da suka sanya hannu a takardun dawo da Sanatan ne kadai hukumar zaben zata tantance a akwatunan zabensu” A cewar kwamishina Mohammed haruna.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, Shugaban hukumar zaben jihar, James Apam ya bayyana cewar za’a bar masu sanya ido domin duba yadda ake aikin tantancewar a dukkan akwatunan yankin.
Ya kara da cewar, akwai akwatuna guda 8 da ba za’a gudanar da wannan atisayen a cikinsu ba, saboda babu wanda yayi korafi daga yankin.
Sai dai kuma, Shugaban hukumar zaben yace ba zasu yadda wani ko wata wakilan jam’iyyu su shigo cikin lamarin ba, inda yace zasu bayyana sakamakon atisayen a ranar 29 ga watan Afrilun.
“Mun kammala dukkan wasu shirye shirye na gdanarda wannan aikin,mun kuma tanadi duk abubuwan da ake bukata domin fara wannan atisayen” A cewar Apam.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya, an zauna tattaunawa na massu ruwa da tsaki na jam’iyyun siyisar dake yankin Dan majalisar da kuma kungiyoyi da jam’iyyun gama kai na yankin da ‘yan jarida da ‘yan sanda da dukkan sauran jami’an tsaro.