
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Katsina ta sanar da kama daya daga cikin ƴan ta’addan da su ka hallaka Hakimin Ƴantumaki, Abubakar Atiku da dogarin sa.
Kakakin Rundunar, Gambo Isah ne ya baiyana hakan yayin da a kai holon ɗan ta’addan da sauran masu laifi a jiya Talata a Katsina.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya tuno cewa tun ranar 1 ga watan Yuni, 2020 ƴan bindiga su ka harba Hakimin.
Sai a ranar 3 ga watan Disamba, 2021 jami’an ƴan sanda su ka sami nasarar cafke Yusif Abdullahi, ɗan shekara 20 daga ƙauyen Kagara da ke Ƙaramar Hukumar Matazu da ke Jihar Katsina.
“A na zargin sa da kasancewa mamba ne shi a gungun ƴan ta’addan da su ka kutsa gidan Hakimin Ƴantumaki Abubakar Atiku su ka hallaka shi.
“Sun harbe Atiku mai shekara 55 tare da dogarin sa, Gambo Isah da daddare.
“A yayin bincike, mai laifin ya amsa laifin sa cewa da shi a ka aikata kisan. Ya kuma ce shi da wasu ƴan bindiga 4 su ka aikata kisan. Ya ce sauran huɗun sun gudu sun ɓuya a cikin daji.
“Yanzu dai a na ci gaba da bincike,” in ji shi.