Home Kanun Labarai Ali Modu Sheriff ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Ali Modu Sheriff ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

0
Ali Modu Sheriff ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyarda ya baro ta APC.

Ana sa ran yau Alhamis Ali Modu Sheriff zai bayyana komawarsa jam’iyar APC a garin Maiduguri.

Ali Modu Sheriff dai ya sha fama da rikici a tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP da ya baro, inda har ya kai karar jam’iyyar kotu, inda daga bisani kotu ta tube shi daga rikon mukamin Shugabancin jam’iyyar na kasa.