Home Labarai Kano: Hisbah ta kama giya an jera ta cikin kwalayen taliya da madara

Kano: Hisbah ta kama giya an jera ta cikin kwalayen taliya da madara

0
Kano: Hisbah ta kama giya an jera ta cikin kwalayen taliya da madara

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta yi nasarar cafke wasu motocin giya, waɗanda a ka yi ɓaddabami a ka shigo da su cikin jihar.

Hukumar ta ce dakarun ta ne da su ke kan sintiri su ka cafke jerin-gwanon motocin, maƙare da barasa a cikin kwalayen taliya, madara, sabulu da sauransu.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa bayan da Hisbah ta samu nasarar damƙe motocin barasar, sai a ka ga cewa a she giyar ce ta gwangwani da ta roba har da ma ta ɗan ƙaramin muzubi, a ka jera su cikin kwalayen a ka manne da salatif, kai ka ce taliya ce ko kuma madara.

Jaridar nan ta kuma jiyo cewa sai da a ka yi ɗauki-ba-daɗi da dakarun Hisbah ɗin kafin su samu nasarar kama motocin, inda har direban ɗaya daga cikin motocin yayi yunƙurin bi ta kan jami’an amma dai su ka samu nasarar damƙe shi.

Bayan sun cafke shi ma sai da gilashin motarsa ya fashe bayan da ya tunkuyi gefen titi domin da ya yi yunƙurin tserewa.

Duk da ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen hana shigowa da barasa cikin jihar, amma abin ya ci tira, domin zai yi wuya mako ya zo ya wuce ba a kama motar barasa an shigo da ita Jihar Kano ba, wacce jiha ce ta Musulmai.