Home Labarai Korona: Yawan talakawan Nijeriya zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 109 a ƙarshen 2022 — Gwamnatin Tarayya

Korona: Yawan talakawan Nijeriya zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 109 a ƙarshen 2022 — Gwamnatin Tarayya

0
Korona: Yawan talakawan Nijeriya zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 109 a ƙarshen 2022 — Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin Tarayya ta baiyana cewa nan da ƙarshen shekarar 2022, yawan talakawan Nijeriya zai iya kaiwa 109.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta baiyana hakan, inda ta ce ƙarin mutum miliyan 11 na iya faɗawa ƙaangin talauci a cikin shekarar 2022, sakamakon annobar korona.

Ahmed ta furta hakan ne a Abuja ranar Talata, a ci gaba da taron da ake yi kan annobar korona mai taken ‘Faɗan ƙarshe wajen yaƙi, tare da murmurewa daga annobar korona’.

Ministar, wacce ta sami wakilcin Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi, Ben Akabueze, ta ce ”Aƙalla mutum miliyan biyu ne suka faɗa talauci a 2020, saboda yadda yawan jama’a ya zarce ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa, annobar ta annobar korona da kuma karyewar tattalin arziƙi sun ƙara yawan wasu matalautan da kimanin miliyan 6.6, lamarin da ya kawo adadin zuwa miliyan 8.6 a cikin shekarar kawai.

“Hakan na nuni da yiwuwar karuwar talakawa a Najeriya daga miliyan 90 a 2020 zuwa miliyan 109 a 2022”. A cewar Ahmed.