
Yayin da su ke fama da aiyukan ƴan ta’adda, al’ummar yankin Ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara, sun sake tura wakili gurin jagoran ƴan bindiga, Turji.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tun a farkon watan Nuwamba ne al’ummar Shinkafin su ka tura wakili domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma sai Turji ɗin ya ƙi amincewa.
Wani mazaunin Shinkafi, Alhaji Ali Mamman ya ce yankin na fama da hare-haren ƴan ta’adda tun bayan da sojojin Nijeriya su ka kaiwa ƴan bindigan hari ta sama, inda yai sanadiyar rasuwar iyaye da ƴan uwan abokin Turji ɗin, Ɗan Bokkolo.
Wani mazaunin kuma ya ce ƴan ta’addan na ci gaba da kai hare-hare a yankin inda ya ƙara da cewa wani lokacin ma sai su kawo hari sau uku a rana.
Amma kuma ya ce mazauna yankin sun fara samun sa’ida tun bayan da a ka girke dakarun tsaro a ranar Litinin.
“Daga cikin wakilan sun haɗa da ƴan ɓangaren Halilu. Da alama dai shi Halilu ne zai shiga tsakani wajen tattaunawar kuma da alama zai yi aiki da wasu mahukunta domin sulhun,” in ji wata majiya ta tsaro.