Home Labarai Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata garkuwa da mutane a kan titin Maiduguri-Damaturu

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata garkuwa da mutane a kan titin Maiduguri-Damaturu

0
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata garkuwa da mutane a kan titin Maiduguri-Damaturu

 

Rundunar Sojin-ƙasa ta Nijeriya ta ƙaryata raɗe-raɗin da a ke yi cewa an yi garkuwa da matafiya a kan titin Maiduguri-Damaturu ranar 11 ga watan Disamba.
Ado Isa, kakakin rundunar haɗin gwiwa ta 7 ta ‘Operation Haɗin Kai’ a arewa-maso-gabas ya baiyana cewa raɗe-raɗi ne maras tushe.
“Mun samu rahoton raɗe-raɗin da a ke yaɗawa a kafafen sadarwa ranar 11 ga Disamba.
“Haka kuma wasu jaridu ma sun buga jita-jitar cewa wai ISWAP sun yi garkuwa da matafiya a Borgozo a Ƙaramar Hukumar Kaga a Borno.
“To wannan jita-jitar ba ta da tushe kuma ana yaɗa ta ne  domin a kushe ƙoƙarin da “Operation Hadin Kai’ ke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƴan Boko Haram ne su ka yi yunƙurin tare hanya a yankin Dole/Bari domin su tada hankalin al’umma.
“Dakarun da ke sintiri da kewaye su ka zo gurin kuma su ka daƙile yunƙurin na su.
“Ba a ɗauke wani matafiyi a ranar Asabar ba, kawai dai aikin ɓatagari da su ke baƙin ciki cewa zan lafiya na dawowa a arewa-maso-gabas,’ in ji Isa, wanda Kanal ne a soja.
Ya kuma jaddada ƙoƙarin da rundunar ke yi na kare  matafiya a titin.