Home Labarai Ramuwar Gaiyya: Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da shigowar jirage daga Canada, Britaniya da Saudiya

Ramuwar Gaiyya: Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da shigowar jirage daga Canada, Britaniya da Saudiya

0
Ramuwar Gaiyya: Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da shigowar jirage daga Canada, Britaniya da Saudiya

p

Da ga ranar 14 ga watan Disamba, Gamwantin Taraiya za ta dakatar da jirage da ga  Canada, Britaniya da Saudi Arebiya da ga shigowa Nijeriya.
Ministan Harkokin Sufurin Jirgin Sama, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a yau Lahadi a Legas.
Sirika ya yi bayanin cewa gwamnati ta sanya takunkumin ne a matsayin ramuwa ga dakatar da jirage da ga Nijeriya da ƙasashen su ka yi sakamakon ɓullar sabon nau’in korona na Omicron.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar nan za ta sanya waɗan nan ƙasashe ukun a matsayin waɗan da za a sanyawa idanu sakamakon ɓullar Omicron ɗin.