Home Ra'ayi RA’AYI: Abinda mu ka zabi Buhari dan shi ya gaza — Hakeem Baba-Ahmed

RA’AYI: Abinda mu ka zabi Buhari dan shi ya gaza — Hakeem Baba-Ahmed

0
RA’AYI: Abinda mu ka zabi Buhari dan shi ya gaza — Hakeem Baba-Ahmed

 

A takaice akwai wadanda sukan rasa abin da zasu ce mani idan na nuna gazawar Shugaba Buhari sai kawai suce ina adawa ne domin bai sa ni cikin gwamnatin sa ba. Wannan ba abin mamaki ba ne, domin abin da ake gaya masu su ce ke nan kawai. Wadanda ke ba su abin fadi basu da abu daya da zasu fada masu su fadi na karya ko sharri akan abubuwan da na kan fada a kan gwamnatin Buhari.

Ni saboda Buhari na shiga siyasa bayan na gama aikin gwamnati a jiha da tarayya, kuma naga yadda gwamnatin Jonathan take daukar mulki ba yadda ya kamata ba, musanman ma matsalolin da suka shafi Arewa. Buri na kawai shine in ba da gudunmuwa a cire Jonathan a samu Buhari ya zama shugaban kasa ya gyara Arewa da Nigeria. Ban taba aiki da Buhari ba, amma kamar miliyoyin mutane, muna da zaton zai iya gyara Nigeria da Arewa da taimakawa talakawa. Na shiga CPC saboda ita ce jamiyyar Buhari a shekarar 2012.

Na zama Chairman na CPC a Jihar Kaduna, da kuma muka hade da AC muka zama APC, aka sake zabe na shugaban APC Jihar Kaduna. Ofis dina a Kaduna shi ne headquarter ta jamiyyar har shekara uku, har sai da na sauka da kaina a shekarar 2014.

A shekarar 2014, General Buhari ya roke ni in taimaka masa in sa ido a dukkan harkokin zabe da abubuwan da suka shafi INEC, kuma na yarda. Na koma Abuja na tsunduma wajen fafutikar neman nasarar APC, kuma Allah Ya amshi addu’ar mu Ya ba shugaban kasa Buhari nasara, kuma muka sami gwamnoni da ‘yan majalisa da yawa, muka kori Jonathan da PDP.

Ni a waje na sai hamdala, buri na na shiga siyasa ya cika.Ban taba sa rai na a mukami ko wani aiki a gwamnatin Buhari ba, ba mu kuma taba maganar bani wani aiki da shi ba. Ni a gani na wanda duk yayi ritaya lafiya, kuma yana da abin da zai tafiyar da iyalin sa, babu wani aikin da zai nema. Aiki daya kawai na roki Allah Ya bani, shine in koma Jami’a in ci gaba da koyarwa kamar yadda nake yi kafin in koma aikin gwamnati. Buhari na zama shugaban kasa na je KASU a matsayin Asso Prof mai ziyara.

Ba’a yi ko shekara daya ba da hawan shugaban kasa Buhari mulki, sai na lura cewa shi mukamin shugaban kasan dama yake so, ba ya yi wa kasa da talaka hankoro ba. Shekaru da nayi na aikin gwamnati shekara 25, (wanda suka hada da rike mukamin Permanent Secretary har shekara 10) sun bani dama in fayyace ingantaccen shugaba da kuma shugaban da bai damu da jamaa ba.

A lokacin ne na yanke shawarar fita daga jaiyyar APC, bayan na shaida wa wadanda da muke APC AKIDA( wato masu neman a dawo hanya) cewa a ganina Buhari da gwamnonin sa basu da niyyar aikin da ya kamata suyi.

Babu gaba ko hamayya tsakanina da Shugaba Buhari da na kusa da shi. Matsalar ita ce ta ko dai in sa ido in yi shiru, ko kuma na ci gaba da abin da ya sa na shiga siyasa, watan taimakawa wajen tsare mutuncin Arewa da jamaar Najeriya, kar iyakan karfi na. Na samu shiga Kundiyar Dattawan Arewa, kuma na gode wa Allah dattawan kirki masu kishin Arewa sun yarda da ni har sun bani mukamin kakakin su.

Na gode wa Allah da ya zabar mani abubuwan da suka fi man amfani, wanda suka hada da kauce wa gwamnatin da yau ake ta kuka da ita a Arewa. Ni dan PRP ne, kuma ban taba zama dan PDP ba. Na yi aikin Chief of Staff na Sanata Bukola Saraki, kuma na gode wa Allah a kan irin samun fahimtar aikin majalisa wanda duk aikin da nayi a da ban samu ba.

Alhamdulillah, Allah Ya albarkaci aikin da muke yi a Kungiyar Dattawan Arewa. Mun yi yakin siyasa na goyon bayan Buhari, kuma yayi nasara.Mun yi wa ‘yan Najeriya kashedi da karawa Buhari wasu shekaru hudu a 2019, amma ba’a ji mu ba. Mun ci gaba da kare mutuncin Arewa, tun lokacin da Buharin ya kan zauna da mu, har yazo idan mun yi magana sai dai a bi mu da munanan maganganu, ko a sa sa’oin jikokin mu su rika zagin mu. A yanzu haka Kungiyar mu sai hamdala, kuma muna rokon Allah Ya bamu magada su ci gaba daga inda zamu tsaya.

Na fadi wannan takaitaccen tarihi ne domin ina ganin ana yaudarar matasa ana masu karerayi a kan mutane irin mu wadanda kan tsaya suce an yi daidai ko ba’a yi ba.Ni a yanzu bana bukatar komi sai ganin karshen irin halin da Arewa ke cikin, da samun mutanen da zasu canji wadannan shugabannin wadanda basu damu da talaka ba.

Ina rokon wadanda kan ji zafin an zage ni, kada su rama. Ni na yafe wa duk mai zagi na ko wani batanci.Ni ma ina rokon gafarar wadanda nayi wa laifi.

Allah Ya iya mana abin da ba za mu iya ba, Ya sa mu bambamta gaskiya daga karya.