
Hukumar Yaƙi da sha da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, NDLEA ta kama wani mai suna Onuoha Friday, ɗan shekaru 43 da ƙwayoyi na tramadol har miliyan ɗaya.
Hukumar ta ce an cafke Friday ne a ranar 10 ga watan Disamba a kan babbar hanyar Legas-Benin.
Mamakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya kuma ƙara da cewa jami’an hukumar sun yi manya-manyan kamu biyu a Anambra inda su ka kama kilogiram 238.973 na miyagun ƙwayoyi.