
Kungiyar Izala ta bayar da umarnin a fara A-ƙunutu a dukkan masallatan Ahlussunnah da ke fadin Najeriya a kan matsalar tsaro.
BBC Hausa ta rawaito cewa ƙungiyar ta wallafa sanarwar ne a shafinta na Facebook a jiya Litinin da rana.
Kungiyar ta Izala ta ba da umarni ga limaman Juma’a da na Kamsu Salawat da sauran dukkan masallatan Ahlussunah da ke fadin Najeriya da a fara gabatar da addu’o’i na Al-Qanut a dukkan masallatai.
Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya ba da umurnin ta hanyar rubutacciyar takarda ga manema labarai kamar yadda sanarwar ta ce
Sheikh Bala Lau ya ce wannan umurni ya shafi duk wani masallaci mallakar kungiyar da sauran masallatan Ahlusunnah dake fadin kasar.
Sanarwar ta ambato Sheikh Bala Lau yana cewa: “Haka zalika dukkan majalis na ilimi da karantarwa da halƙoƙi na ilimi da haddar Al Qurani Mai girma da duka nau’uka na addua, duka muna ba da ummurni a ci gaba da yin addu’o’i.
“Haka ma mata a gida su ma su bi wannan umarnin da yawaita azkar da fatan Allah ya tausaya wa wannan al’umma.
“Idan mun yi wannan da kyakkyawar niyya muna zaton Allah zai amsa mana ya yi maganin ƴan ta’adda da masu daukar nauyinsu, kuma za a samu zaman lafiya a yankunan da matsalar tsaro ta shafa insha Allah,” in ji shi.
Shugaban na Izala ya ce wannan mataki zai fara aiki ne nan take ba tare da jiran komi ba.
Sanarwar ta rufe da addu’ar “Allah ya mana jagora, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa. Amin.”