
Hausawa dai su ka ce “Allah ɗaya, gari bamban”. Yayin da likitoci ke kira da a riƙa yin murmushi da dariya domin gujewa kamuwa da ciwon hawan jini da damuwa, Ita kuwa Gwamnatin North Korea hana dariyar ta yi.
Duk wanda a ka ga fuskarsa akwai alamar farin ciki, to kuwa zai ɗanɗana kuɗarsa a ƙasar.
Gwamnatin North Korea ta saka wannan zazzafar dokar ne domin yin jimamin cika shekaru 10 da rasuwar shugaban ƙasar, Kim Jong-il.
Jaridar The Telegraph ta rawaito cewa an kuma hana yin dariya da shan barasa har tsawon kwanaki 11 na jimamin tunawa da rasuwar tsohon shugaban ƙasar.
Gobe 17 ga watan Disamba, shine daidai shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-il, kuma da ga goben za a hana ƴan North Korea ɗin zuwa yin siyaiya a kantuna.
“A lokacin yin jimamin, an hana mu yin dariya, shan giya ko kuma yin wasu abubuwa na farin ciki,” in ji wani ɗan North Korea da ke Arewa-maso-Gabas da bodar Sinuiju yayin da ya ke shaidawa gidan rediyon Radio Free Asia (RFA).
“Ko da ma wani ya rasu a dangi a cikin kwanakin jimamin, to ba wanda ya isa ya yi kuka a baiyane kuma ba za a binne gawar ba sai bayan kawankin jimamin. Idan kuwa ranar haihuwar mutum ta faɗo cikin kwanakin jimamin, to fa sai dai a hakura don ba za a yi bikin zagayowar ranar haihuwa ba,” in ji shi.
Kim Jong-il, wanda ya mulki ƙasar da ga shekarar 1994 zuwa shekarar 2011 lokacin da ya rasu sakamakon ciwon zuciya, shine mahaifin Shugaban Ƙasar na yanzu, Kim Jong-un.
Kim Jong-il ya mulki ƙasar tsawon shekaru 17 kafin rasuwarsa a shekarar 2011.