Home Ilimi Tsoffin ɗaliban BUK sun bada N500,000 tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi

Tsoffin ɗaliban BUK sun bada N500,000 tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi

0
Tsoffin ɗaliban BUK sun bada N500,000 tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi

 

Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Bayero Kano, BUK, aji na shekarar 1989, sun baiwa jami’ar naira dubu 500 domin tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi ƴan asalin Jihar Kano.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Kabiru Jinjiri Ringim ne ya baiyana hakan yayin da ya jagoranci wasu mambobin ƙungiyar zuwa ziyara ga Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas a ofishin sa a jiya Juma’a.
Dakta Jinjiri ya ce “ƙungiyar ta tanadi tsare-tsare duk shekara a ƙoƙarin ta na tallafawa marasa ƙarfi, musamman a ɓangaren ilimi,”
A jawabin shi, Shugaban na BUK, Farfesa Abbas ya yabawa ƙungiyar bisa wannan abin alheri da ta yi.
Ya ƙara da cewa a ƙoƙarin ta na tallafawa ɗalibai ƴan jihar, jami’ar ta ɓullo da wani tsari na ɗaukar aiki, inda jami’ar ta ɗauki ɗalibai 125 aiki na wucin-gadi a karon farko.
Shugaban makarantar, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na ɓangaren aiyukan gudanarwa, Farfesa Mahmud Umar Sani ya ce tsarin wani yunƙuri ne na tallafawa ɗalibai da kuma rage musu raɗaɗin fatara.
Ya kuma ƙara da cewa tallafin da kungiyar tsoffin ɗaliban ta bayar ya zo a daidai lokacin da a ke buƙatarsa.