
Motar gingimari ta murƙushe wani jami’in Hukumar Kare Haɗarurruka ta Ƙasa, FRSC, har ya rasu a titin Sagamu-Ijebu Ode a Jihar Ogun, kamar yadda Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito.
Kwamandan hukumar na jihar ne ya shaidawa NAN a yau Laraba a Abeokuta, inda ya ce haɗarin ya faru ne a ranar Litinin.
Umar ya baiyana cewa haɗarin ya faru ne sakamakon ganganci da kuma gudun wuce sa’a da direban motar ya ke yi.
“Direban me yanke ganganci kuma ya na gudun da ya wuce kima, a haka ne har ya kasa amfani da birki, Shine shine har ya buge jami’in namu.
“Lokacin jami’an mu na tsaye a jikin motar mu ta sintiri, kwatsam sai ga wannan gingimari ta taho, kawai sai ta doke jami’in mu ta haɗa shi da jikin motar mu ta sintiri, inda ya ce ga garinku nan, sannan ɗaya jami’in namu yanki rauni,” in ji Ahmed.
Ya ƙara da cewa direban motar ya tsere bayan ya buge jami’in namu, amma jami’an mu su ka bishi tare da masu motoci da baburan da abin ya faru a kan idon su har su ka samu nasarar kamo shi.
“Sun bi shi, sai ya sauka da ga motar ya tsere. Nan fa su ka ci gaba da binsa har su ka cafke shi, inda muka tuni mun miƙa shi a hannun ƴan sanda,” in ji shi.
Kwamandan ya ƙara da cewa jami’in da ya samu rauni na asibiti ya na karɓar magani.