Home Labarai Sarauniyar Kyau: Ba mu ce za mu gaiyaci Shatou da iyayenta ba — Hisbah

Sarauniyar Kyau: Ba mu ce za mu gaiyaci Shatou da iyayenta ba — Hisbah

0
Sarauniyar Kyau: Ba mu ce za mu gaiyaci Shatou da iyayenta ba — Hisbah

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta musanta rahoton cewa ta na shirye-shiryen gaiyatar Sarauniyar
Kyau, Shatou Garko da iyayenta.

Babban Daraktan Hukumar, Dakta Aliyu Musa Aliyu Kibiya ne ya baiyana hakan ga manema labarai a jiya Laraba.

Ya ce, ba su gaiyaci Shatou da iyayenta ba, tambaya ce kawai a ka yi wa
Kwamandan hukumar, Malam Harun Ibn Sina, shi kuma ya yi nasiha.

“Babu wani umarni da mu ka bayar na a gaiyato ta ko iyayenta. Labari ne na
ƙanzon kurege”, a cewarsa.

Ya ce Hisbah ta yi nasiha ne kan baiyana tsiraici wanda haramun ne a addinin Musulunci.

Ko da Daily Nigerian Hausa ma ta tuntuɓi Kakakin Hisbah na Kano, Lawal Ibrahim Fagge, shima ya musanta batun gaiyatar, in danya ce”tun ranar Litinin rabon da Kwamanda ya samu zama a ofis, shima kuma Babban Darakta ya ce bai san da maganar gaiyatar ba,”

Idan an tuna, a makon da ya gabata ne aka zaɓi Shatou Garko, ƴa4 asalin Jihar Kano a matsayin sarauniyar kyau a
wani taro da aka yi a birnin Legas.

Sai dai wannan zaɓe ya samu martani daga al’umma, kasancewar ita ce ƴar
Kano ta farko da ta taɓa samun wannan matsayi.