
Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ƙaddamar da titin Ado-Iyin mai ruɓi biyu, wanda tun lokacin sojoji, a shekarar 1978 a ka bada kwangilar aikin amma sai a ka banzatar da shi.
Fayemi ya ce gwamnatocin sansu ka zo a baya ne su ka banzatar da titin, wanda a farkon kwangilar, mai hawa ɗaya ne da ya tashi da ga Iyin zuwa Igede-Aramoko da wani yanki na Jihar Osun.
A jawabin sa yayin ƙaddamar da aikin, Fayemi ya ce ya yi farin ciki da kammala aikin da ya daɗe ya na ci wa mutanen yankin tuwo a ƙwarya.
Ya kuma ƙara da cewa titin zai samar da sauƙin zuwa tsakanin babban birnin jihar da kuma Iyin Ekiti.
Gwamnan ya baiyana cewa za a sanya kofar karbar kudi a titin, in danya ce titin zai bunƙasa tattalin arzikin jihar domin zai saukakawa ƴan kasuwa da mai ana su riƙa dakon kaya na tare da wata wahala ba.
Ya ce yanzu dai an kammala kashi na farko na aikin, inda a ka maida shi mai ruɓi biyu kuma a ka sanya masa fitilu.
Fayemi ya ci alwashin kammala duk sauran aiyukan da gwamnatocin baya su ka ƙasa kammalawa.