
Daga Hassan Y.A. Malik
Fitaccen dan wasan tsakiya na kungiyar Barcelona da tawagar kwallon kafa ta Spaniya, Andres Iniesta ya bayyana cewa zai bar kungiyar ta Barcelona da ya ke a matsayin kyaftin dinta a karshen kakar wasannin da muke ciki.
Iniesta ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka gudanar don tattauna bankwana da dan wasan mai shekaru 33 a jiya Juma’a.
Dan wasan ya bayyana cewa zai bar Barca, kuma zai ci gaba da murza leda amma ba zai shiga kungiyar da ta ke a nahiyar turai ba don gudun kar watan wata rana ya kara da Barcelona.
Kodayake Iniesta bai bayyana kungiyar da zai koma ba, amma ya jaddada cewa babu wani dalili da zai sanya ya fuskanci Barcelona a wasan kwallon kafa a sabuwar kungiyar da zai koma.
“Abu ne mai matukar wuya yin bankwana da kungiyar da shafe kafatanin rayuwata ina murzawa leda.”
“Ni da duk abinda na zama a rayuwa, Barca ce sanadi, saboda haka ina matukar godiya.”
“Zuwa yanzu kungiyoyi, masu horaswa da ma ‘yan wasa na kungiyoyi da dama sun tuntube ni kan batun ko zan koma wata kungiyar da suke da bukata na koma, amma a zahirin maganar gaskiya ba zan iya komawa wata kungiyar da zata iya karawa da Barca ba. Wannan shi ne gaskiyar zance.”