Home Siyasa 2023: Ba na neman kujerar gwamnan Kano — Makoɗa

2023: Ba na neman kujerar gwamnan Kano — Makoɗa

0
2023: Ba na neman kujerar gwamnan Kano — Makoɗa

 

Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Ali Haruna Makoɗa ya baiyana cewa bashi da burin tsayawa takarar kujerar gwamnan Kano a zaɓen 2023.

Makoɗa ya ƙara da cewa shi ba ya neman wata kujerar mulki a shekarar zaɓe ta 2023.

An daɗe a na raɗe-raɗin cewa Makoɗa na cikin ƴan siyasar da su ke harin babbar kujerar mulki a Kano idan kakar zaɓe ta 2023 ta zo.

Makoɗa, wanda tsohon Kwamishinan Muhalli na Jiha ne, ya baiyana hakan a yayin da ya ya ke gabatar da jawabi a wajen taron Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makaranatar Sakandire ta Kafin Hausa, ƴan aji na shekara 1988.

Ya ce “Ali ba ya neman wata kujerar mulki a shekara ta 2023 sai kujerar da Allah ya zaɓa masa, wadda za ta zama alkhairi a gare ni da ku da duk al’ummar Jihar Kano baki ɗaya, tun da zaɓin Allah shi ne dai-dai,”

Dakta Makoɗa ya roƙi ‘ya’yan ƙungiyar da su taya su da yin addu’o’in kammala aikin da aka ɗora musu lafiya kamar yadda su ka fara lafiya.

Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa masoya Makoɗa sun daɗe su na kiraye-kirayen ya fito neman kurejar gwamnan Jihar Kano, sabo da irin gudunmawar da su ke ganin zai iya bayarwa wajen cigaban jihar idan ya samu dama.