
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, NFF ta sanar da naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasa wato Super Eagles a yau Laraba.
Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa sanar da naɗin sabon kocin na ƙunshe ne a wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na NFF, Ademola Olajire ya fitar.
A cewar sa, mahukunta a NFF ne su ka sahale ɗaukar Peseiro a matsayin koci a ganawar yanar gizo da hukumar ta yi a yau Laraba domin tattauna muhimman batutuwa a kan kwallon kafar Nijeriya.
Sai dai kuma Olajire ya baiyana cewa sai bayan gasar cin kofin Nahiyar Afirka wacce za a yi a ƙasar Kamaru sannan sabon kocin zai kama aiki.