Home Labarai YANZU-YANZU: Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan fashin daji Kachalla da Auta a Zamfara

YANZU-YANZU: Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan fashin daji Kachalla da Auta a Zamfara

0
YANZU-YANZU: Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan fashin daji Kachalla da Auta a Zamfara

 

Ƙasurguman ƴan ta’adda masu fashin daji, Alhaji Auta da Kachalla Ruga sun rasa rayukansu a yayin wani hari da a ka kai musu a daji a Jihar Zamfara, kamar yadda jaridar PRNigeria ta tabbatar.

Kwamandojin sun gamu da ajalinsu ne a juya da daddare bayan da Rundunar Sojin Sama, NAF, ƙarƙashin ‘Operation Hadarin Daji’, ta yi musu luguden wuta ta jiragen yaƙi a dajin Gusami da ke ƙauyen Tsamre da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji a jihar ta Zamfara.

PRNigeria ta jiyo cewa hare-haren da a kai ta jiragen yaƙi a safiyar yau asabar ya yi sanadiyar hallaka yaran Auta da Kachalla da dama a dajin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa su ma sauran ƴan fashin daji da su ka taru a gidan Auta domin yi masa jana’iza, sun haɗu da ajalinsu, inda jiragen yaƙin su ka yi musu luguden wuta ta sama, kuma su ka hallaka da dama da ga cikin su.

Wata majiyar soji ta shaidawa PRNigeria cewa maimai ɗin harin da rundunar ta kaiwa sauran ƴan fashin dajin da su ka tsere da wadanda su ka laɓe ƙarƙashin bishiyoyi su mana sun gamu da gamon su, inda a ka hallaka da dama da ga cikin su.