
Rahotanni sun baiyana cewa a ƙalla mutane 18 ne, har da mata ƴan ta’adda su ka yi garkuwa da su a Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.
Rahotannin sun baiyana cewa ƴan ta’addan kuma sun bindige mutum ɗaya.
An ce ƴan ta’addan sun dira a garin ne wanda ya ke kan hanyar Kaduna zuwa Barinin Gwari da misalin ƙarfe 12:30 na safe a yau Lahadi.
Wani sannen mutum a garin Udawa, Muhammad Ummaru ya tabbatar da cewa an kashe mutum ɗaya mai suna Bala Jaja.