
Rundunar ƴan sanda a Jihar Zamfara ta ce ta damƙa wasu ƙananan yara 21 da ta kuɓutar, bayan mahaifansu sun tura su zuwa karatun allo amma sai ƴan fashin daji su ka tare motarsu cikin dare a ƙarshen mako.
Ta ce ƙananan yaran sun fito ne daga ƙaramar hukumar Bakura a kan hanyarsu ta zuwa Ɗan Dume cikin jihar Katsina mai maƙwabtaka, kafin sace su a ranar Juma’a.
Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai sama da 1000 a cikin shekarar da ta yi bankwana akasari a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja.
‘Ƴan bindiga sun sace fasinjoji daga motoci goma a Zamfara’
Zamfara: Nasarorin da ƴan sandan jihar suka ce sun samu cikin wata daya.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya faɗa wa BBC Hausa cewa ranar Juma’a daliban su 19 da mata biyu ” sun kawo daidai dajin Kucheri ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.”
Ya ƙara da cewa wasu mutane ne suka bulguta ma hadakar jami’an tsaron yankin wadda ba ta yi wata-wata ba ta tunkari barayin ta kwato su.
SP Muhammad Shehu ya kuma tabbatar da cewa babu ko da yaro daya daga cikinsu da ya samu rauni ko wata matsala yayin artabun, kuma an kubutar da su duka.
Da BBC ta tambaye shi halin da suke ciki sai ya ce “suna cikin koshin lafiya domin an duba lafiyarsu babu wani wanda ke cikin wani yanayi na rashin lafiya.”
“Mun kira jami’an karamar hukumar mulkin Bakura kuma an hannata musu wadannan yaran don mika su ga iyayensu.” Inji SP Muhammad Shehu.
Sai dai ya yi gargadin cewa al’umma su daina tafiyar dare, kasancewar masu satar sun fi ayyuka a lokacin.
Yan awanni kafin sace daliban ranar Juma’a, maharan sun buda wuta a daidai kauyen na Kucheri, inda suka kashe mace daya suka kuma yi garkuwa da matafiya daga motoci 10.