
Wasu bayanai sun ƙara fitowa cewa sabon nau’in korona na Omicron na kama saman hanyar numfashi, inda ta ke haifar da alamu ba masu zafi ba kamar nau’o’in cutar na farko, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO a yau Talata.
“Mu na samun karin bayanai da shaidu cewa Omicron na kama sassan dan’adam da ga sama.
“Ba kamar nau’o’in cutar na baya ba,” Abdi Mahamud, Manaja a WHO ya sahidawa ƴan jarida a birnin Geneva.
Ya ƙara da cewa “hakan ka iya zama labari ne mai daɗi.”
Amma kuma ya ce yadda cutar ke tafiya kamar wutar daji, za ta mamaye gurare da dama a fadin duniya, inda hakan zai zama barazana ga ƙasashen da su ke da mutane da dama da ba su yi rigakafin korona ba.