
Ƴan vigilante, wanda a ke kiransu da Ƴan Sakai a Jihar Zamfara sun hallaka wasu da a ke zargin masu shunen mutane ne ga ƴan fashin daji a jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an hallaka 11 da ga cikin su a ƙauyen Gada da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu, inda 4 kuma a ka bazar da su a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
Rahoton ya ƙara da cewa ƴan vigilante ɗin sun yi wa waɗanda a ke zargi ɗin ƙawanya a kasuwar wayar salula da ke garin Ƙauran Namoda.
An kama waɗanda a ke zargin, inda ba su daɗe ba kuma ba tare da wata-wata ba a ka hallaka su kusan mako ɗaya da kai wani mummunan harin ƴan ta’adda a garin.
A harin, an kashe dagacin garin da wasu mutane biyar, inda ƴan ta’addan su ka kaɗa mata da ƙananan yara zuwa jeji.
Tun da fari, Ƴan Sakai ɗin sun sun dira wani gari mai suna Tuskudu, wani ƙauye ne mai tsawon kilomita 1 da ga garin Gada, domin neman masu shune.
Mazauna garin sun ce wani mai suna Ada an gan shi ya na nuna gidajen da za a kai hare-haren.