
Ƙungiyar Ma’aikatan Ofishin Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila (Gbaja Professinals Volunteers Network ) da haɗin gwiwar Ƙungiyar Malaman Gaba da Sakandire ta Yankin Dawakin Tofa sun Ɗauki nauyin karatun ɗaliban yankin har su 130, tun daga matakin firamare.
Shugaban ma’aikatan ofishin shugaban majalisar, Sunusi Garba Rikiji, wanda ya wakilci Shugaban, ya bayyana cewar wannan tsari somin-taɓi ne, domin za su cigaba da aiwatar da shi a sassa daban-daban da ke faɗin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewar Shugaban majalisar kullun zuciyarsa a baiyane ta ke wajen ɗaukar Nijeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa baki ɗaya, shi ya sa kullum ya ke ƙoƙarin aiwatar da shirin tallafawa karatun ƙananan yara a kowanne yanki a ƙasar nan.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Ado Tambai Ƙwa, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Garba Yusif Labour ya nuna farin cikinsa bisa tallafin.
Ya bayyana gamsuwarsu da irin wannan gudummuwa da su ka samu, inda ya kuma ja hankalin Slsauran al’umma masu riƙe da madafun iko da su yi koyi da wannan kyakkyawan tsari.
A ƙarshe, Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Isma’il Umar Ganduje ya baiyana jin daɗinsa bisa wannan abin alheri, tare da fatan al’ummar da su ka taru a wajen ƙaddamarwar sun koma gida lafiya.