Home Labarai Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Dakta Ahmad Bamba ya rasu

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Dakta Ahmad Bamba ya rasu

0
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Dakta Ahmad Bamba ya rasu

 

Rahotanni da ga Jihar Kano sun baiyana cewa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, wanda ya yi fice a fannin Hadisi, Dakta Ahmad Muhammad Bamba, ya rasu.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa iyalan marigayin ne su ka sanar da rasuwar ta sa a yau Juma’a.

Wannan jaridar ta jiyo cewa Dakta Ahmad, wanda ya ke koyarwa a Jami’ar Bayero Kano, ya rasu ne a yau Juma’a a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.

Marigayin, a cewar majiyoyi da ga iyalin sa, ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya kuma kwana ɗaya tak ya yi a asibiti.

Za a yi jana’izar Marigayin bayan sallar juma’a a Masallacin sa na Darul Hadis da ke Unguwar Tudun Yola a birnin Kano.

Jihar Kano dai ta fuskanci rasuwar fitattun mutane, inda ko a Litinin ɗin da ta gabata fitaccen ɗan siyasar nan kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Bashir Othman Tofa ya rasu.

Hakazalika, a makonnin da su ka gabata ma Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Muslunci, Dakta Ibrahim Datti Ahmad ya rasu.