Home Labarai Ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya: Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya

Ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya: Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya

0
Ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya: Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya

 

A yau Juma’a ne Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe duk titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya da na Maikatar Harakokin Waje a Abuja.

Shugabar Ma’aikata na Taraiya, Dakta Folasade Yemi-Esan ce ta bada umarnin a yau a wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar, Abdulganiyu Aminu ya fitar.

A cewar Yemi-Esan, rufewar ta biyo bayan bikin tunawa da ƴan Mazan jiya na 2022.

Sanarwar ta ce a bikin, wanda z a yi a gobe Asabar, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da sauran jami’an gwamnati za su je a gurin bikin domin karrama ƴan Mazan Jiya da su ka rasa rayukansu a wajen yaƙi.

Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa a kowacce ranar 15 ga watan Janairu, rana ce ta bikin tunawa da sojojin Nijeriya da su ka rasu a wajen yaƙi da wasu ƙasashen.