Home Labarai Ƴan Sanda sun kama masu ci da sayar da naman ɗan’adam a Zamfara

Ƴan Sanda sun kama masu ci da sayar da naman ɗan’adam a Zamfara

0
Ƴan Sanda sun kama masu ci da sayar da naman ɗan’adam a Zamfara

 

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta ce ta kama mutum huɗu da zargin ci da kuma sayar da sassan jikin ɗan’adam, wani abu da ba a saba gani ba a jihar.

A taron manema labarai da ya gudanar a Gusau babban birnin jihar a jiya Alhamis, Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Ayuba Elkanah ya ce an damƙe waɗanda a ke zargin ne bayan da jami’an tsaro su ka tsinci gawa a wani kango, ba tare da wasu sassan jikinta ba.

Elkanah ya ce gano gawar wani ɓangare ne na bincike da a ke yi kan ɓatan wani yaro ɗan shekara 9 da haihuwa.

Ya ƙara da cewa, tun a makon da ya gabata ne a ka ma mutane huɗu da a ke zargi, da suka haɗa da wasu magidanta maza biyu da kuma matasa suma maza biyu.

Ya ƙara da cewa yanzu haka ana kan neman wasu mambobin ƙungiyar da a ke zargi da cin naman mutane.

Kazalika kwamishinan ƴan sandan ya ce kawo yanzu, bincike ya nuna cewa sau biyu shugaban ƙungiyar na tura wa uku daga cikin waɗanda a ka kama naira dubu 500 na cinikin sassan jikin dan’adam.

Cin nama da sayar da sassan jikin mutane wani sabon abu ne a Zamfara, duk da jihar ta yi ƙaurin suna wurin kashe-kashe da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa daga ƴan bindiga tsawon shekaru.

Kuma hukumomin Najeriya na shan suka saboda nuna gazawa wurin shawo kan halin da jihar ke ciki.

A wata mai kama da haka yayin zantawa da manema labaran CP Ayuba Elkana ya ce jam’ian tsaro sun kubutar da mutun 17 da aka sato daga jihar Neja aka shiga da su Zamfara.

Ya kara da cewa yayin wani sintiri, ‘yan sanda sun ƙwato makamai da suka hada da bindigar harba makamin roka, bayan bata kashi da ‘yan bindiga a wani daji da ke yankin.