Home Wasanni AFCON 2021: Nijeriya ta lallasa Sudan 3-1

AFCON 2021: Nijeriya ta lallasa Sudan 3-1

0
AFCON 2021: Nijeriya ta lallasa Sudan 3-1

 

Tawogar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya, Super Eagles ta lallasa takwararta ta Sudan da 3-1 a gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin Afirka, AFCON ta 2021.

Tun a minti na 2:18 da take wasa, ɗan wasan gaba, ya fara jefa wa Nijeriya ƙwallo.

Da ga nan kuma a minti na 45, sai Taiwo Awoniyi ya ƙara ƙwallo ta 2.

Bayan minti ɗaya da jefa ƙwallo ta biyun ne sai kuma Moses Domin ya zura ta 3 a gidan koma.

A minti na 70 me su ma Sudan ɗin su ka jefa ƙwallo ɗaya tilo ta bugun da ga kai sai mai tsaron gida, inda a ka tashi 3-1.

Yanzu dai sakamakon ya baiwa Nijeriya nasarar kaiwa zagaye na gaba a gasar.

A ranar 19 ga watan Janairu ne Nijeriya za ta yi wasan ta na ƙarshe a zagaye rukuni na gasar, inda za ta kara da Guniea-Biassau da ƙarfe 8 na dare a agogon Nijeriya.