Home Labarai Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 5 yayin da ƴan ISWAP ke yunƙurin shiga Biu

Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 5 yayin da ƴan ISWAP ke yunƙurin shiga Biu

0
Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 5 yayin da ƴan ISWAP ke yunƙurin shiga Biu

 

Rundunar Sojin Ƙasa ta ‘Operation Hadin Kai’ ta ce ta lallasa ƴan Boko Haram da ISWAP.
Sojojin sun lallasa ƴan ta’addan ne yayin da su ke yunƙurin kurdawa cikin garin Biu a Jihar Borno.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojin Ƙasa, Onyema Nwachukwu shine ya baiyana haka a wata sanarwa a yau Lahadi.
Ya ce sojojin runduna ta 231 da 331, ƙarƙashin sashe na 2 ne su ka fatattaka yan ta’addan.
Ya ce ƴan ta’addan sun gamu da gamon su ne yayin da sojoji su ka dirar musu sanda su ke yunƙurin shiga garin Biu ta ƙauyen Maina Hari village in Biu a jiya Asabar.
Ya ce sojojin sun gwada kwanjin su a kan ƴan ta’addan har su ka hallaka 5 da ga cikin su, in da su ka fatattaki sauran.
Ya ce kuma sojojin sun kwace kayan yaƙi iri-iri a hannun ƴan ta’addan.