
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa Ahmadu Haruna Ɗanzago, Shugaban Jam’iyar APC ɓangaren Shekarau ziyarar ta’aziyar rasuwar ɗan uwansa a yau Lahadi a Kano.
Mai taimakawa Ganduje a kan Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, Abubakar Ibrahim ne ya baiyana hakan.
Ya ce Ganduje ya kai ziyarar ne tare da kwamishinonin sa da sauran ƴan siyasa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Ɗanzago sun samu bambancin siyasa da Ganduje kwanaki kaɗan bayan da a ka kammala zaɓen shugabancin jam’iya na jiha.
Da ga bisani rikicin ya kai su ga zuwa kotu, inda ɓangaren da Ɗanzago ya ke, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, su ka samu nasara, da ga bisani tsagin Ganduje su ka ɗaukaka ƙara.