
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tabbatar wa da iyayen Hanifah cewa zai taimaka musu wajen ganin cewa an bi musu haƙƙin ƴar su.
Kwankwaso ya bada tabbacin ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga mahaifan Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 da malamin ta ya yi mata kisan gilla a Kano a jiya Lahadi.
Kwankwaso ya yi addu’ar neman rahma ga Hanifah, in da ya roƙi Allah da ya baiwa mahaifan nata hakuri da juriya a kan ibtila’in da su ka tsinci kansu a ciki.
Tsohon Gwamnan ya tabbatar musu da cewa duniya baki daya na tausaya musu a bisa kisan gillar da a ka yiwa ƴar su ƙwaya ɗaya tilo, inda ya shaida musu da cewa za a bi diddigin lamarin har sai an tabbatar da bi musu haƙƙin ƴar ta su.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kwankwaso ya samu rakiyar ɗan takarar gwamnan Kano na PDP a zaben gwamna na 2019, Abba Kabiru Yusuf da sauran muƙarraban sa.