
Daga Hassan Y.A.Malik
‘Yan sanda sun damke wata ‘yar aiki bayan da ta ji wa maigidanta mummunan rauni a yayin da ya ke yunkurin yi mata fyade.
Wannan lamari ya faru ne a kasar Uganda.
‘Yar aikin mai suna Nakayanga Rashida ta kwada wa maigidan nata dutse ne a ka, lamarin da ya sanya shi ya yi ta zubda jini.
Yayin da ‘yan sanda suka sanya mata ankwa, Rashida ta yi ta zubar da hawaye ta na rokon a yafe mata, kamar yadda rahotan ya bayyana.
To, sai dai babu batun ko ‘yan sandan sun kama maigidan da yunkurin fyade ko kuwa kyale shi suka yi.