
Daga Hassan Y.A. Malik
Wani bawan Allah mai kimanin shekaru 33, mai tsananin zafin kishi, da aka bayyana sunansa da Lukman Madotti, ya watsa wa budurwar da zai aura ruwan ‘acid’.
A sakamakon aikata wannan laifi, an gurfanar da shi a kotun Majistare da ke Ebute Metta inda ake tuhumarsa da laifin yunkurin kisa.
‘Yar sanda mai shigar da kara a gaban kotu, ASP Clara Adegbayi, ta fada wa kotu cewa saurayin ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Afrilu da misalin karfe 6 na safe a gida mai lamba 11 da ke kan titin Lasisi, Idi-Oro, a yankin Mushin da ke jihar Legas.
Ta ce Lukman ya watsawa budurwar ta shi mai suna Muyiba ‘acid’ din ne a sakamakon zarginta da ya ke yi da neman wani saurayi daban.
Laifin ya saba wa dokar Jihar Legas ta shekarar 2015.
Kamfanin dillancin labaran NIjeriya NAN ya rawaito cewa irin wannan laifi na da hukuncin daurin rai-da-rai a karkashin wannan doka.
An daga sauraren karar zuwa ranar 4 ga watan Yuni.