Home Labarai Matashi ya kashe kansa saboda ya rasa aikin yi

Matashi ya kashe kansa saboda ya rasa aikin yi

0
Matashi ya kashe kansa saboda ya rasa aikin yi

Daga Hassan Y.A. Malik

Wani nakasasshen saurayi mai shekara 24, ya hallaka kansa a sakamakon kasa samun aikin yi da ya yi a jihar Ebonyi.

Saurayin mai suna Awoke Onuabuchi ya hallaka kansa ne ta hanyar shan maganin bera da yammacin ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Amma sai da safiyar ranar Litinin aka samu gawarsa.

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa saurayin ya taba rasa hannunsa na dama a wani hatsarin mota da ya yi a 2016.

Onuabuchi, wanda ya gama karatunsa na sakandare, dan garin Agalegu ne, a karamar hukumar Ikwo da ke jihar Ebonyi.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Loveth Odah, ya ce ‘yan sanda sun sami sauran maganin beran da Onuabuchi ya kwankwada.

Tuni dai aka kai gawar dakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da bincike.