
Daga Jaafar Jaafar
Ga dukkan alamu, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya sallata a fadan da ya ke jagoranta a jam’iyyar APC ta Kano.
Sai dai abin da wasu ba su sani ba shi ne, Malam Shekarau tamkar haƙoran gaba ne a cikin rigimar- kwalliya kawai aka jawo shi a yi da shi ba tauna ba.
Hon. Shaaban Sharada kusan shi ke rike da jam’iyyar a tsagin Danzago tun daga mazabu har matakin jiha. Shi da Sanata Barau Jibrin da Hon. Tijjani Jobe ne su ka kashe miliyoyin nairori don biyan lauyoyi. Su suka jagoranta, kuma suka dauki nauyin kwangires a mazabu da kananan hukumomi. Sha’aban ne ya yi shige-da-ficen da har uwar jam’iyya ta karbi sakamakon kwangires na tsagin su.
A farko rigimar ta fara ne saboda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai jawo wasu jigajigai a jam’iyyar a jika ba, amma a yanzu ana yin rigimar ne kan takarar gwamna a zaben 2023.
Sha’aban ya dauko rigimar ne bayan an sutale shi a karamar hukumarsa ta Municipal. Amma a halin yanzu ya rike wuta a rigimar ne saboda yana da niyyar takarar gwamna. Hon. Tijjani Jobe shi ma ya shiga rigimar ne saboda makomar siyasarsa a 2023, domin ɗan gwamna, Abba Ganduje ya nuna ya na sha’awar kujerarsa. Haka shi ma Sanata Barau Jibrin ya shiga rigimar ne don bukatar takakar gwamna da ya ke so, kuma da yadda ya lura bakin gwamnan ya fi karkata wajen babban abokin hamayyarsa, Murtala Sule Garo.
Amma fa Gwamna Ganduje kusan duk shi ya jefa kansa a wadannan rigingimun. Kuskure na farko shi ne, rashin tsakurawa sanatoci da ‘yan majalisu kaso na ƴan takara a zaɓen shugabannin jam’iya da kuma yadda ake zargin cewa ya baiwa Murtala Garo damar ya dama kowa ya sha, kuma ya dinka kowa ya daura a kasafin mukaman jam’iyya. Wannan kam ya hasala jigajigan jam’iyyar ta APC kuma ya sa guna-guni a tsakanin su.
Kuskure na biyu shi ne, yadda gwamna ya biye wa ‘yan zuga su ka farraka tsakaninsa da Shaaban, duk da cewa yana cikin wadanda su ka yi kai-komo a fadar Shugaban Kasa a yayin da ake kokarin dakile takarar gwamnan a zaben 2019. Mece ce karamar hukuma daya a cikin arba’in da hudu da ke Kano?
Kuskure na uku shi ne yadda Gwamna Ganduje ya yi buris, ya ki gani da daukar wayar tsohon Gwamna Mallam Shekarau a lokacin da Sanatan ya ke neman a tsakura masa kaso a lokacin zaɓen shugabannin jam’iya. Kai har Dubai sai da Shekarau ya bi Ganduje don ya samu ya gan shi, amma duk da haka gwamnan ya zulle ya ki ganin shi.
Hausawa na cewa idan loma daya ta ishi makwalanci, to a tsoma a mai a ba shi. Da Ganduje ya tsakura musu loma-loma, watakil da ba ta kai shi ga zama teburin sulhu da su Shekarau da Barau da Sha’aban da sauransu ba. Abin tausayawa ne ga Ganduje, wai takwaransa na Zamfara (wanda ya shigo jam’iyyar jiya, kuma uwar jam’iyya ta ba shi komai dungurugun a jiharsa) shi zai jagoranci rabon mukaman jam’iyya a Jihar Kano.
Ba na zaton wannan sulhun mai kama da dodorido zai dore, domin babu tsagin da zai janye kararsa saboda wannan sulhun, kuma babu tsagin da idan bai yi nasa a kotun daukaka kara ba, zai hakura da zuwa kotun koli.
Mu na ji, mu na gani, muna kuma sauraro.