Home Labarai Wanda ake zagi da kashe Hanifa ya roƙi Gwamnatin Kano da ta ɗaukar masa lauya

Wanda ake zagi da kashe Hanifa ya roƙi Gwamnatin Kano da ta ɗaukar masa lauya

0
Wanda ake zagi da kashe Hanifa ya roƙi Gwamnatin Kano da ta ɗaukar masa lauya

 

Abdulmalik Tanko, Malamin Makarantar Noble Kids School, wanda a ke zargi da sacewa da kuma kashe ɗalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, a Jihar Kano, ya nemi Gwamnatin Kano da ta ɗaukar masa lauya da zai kare shi a kotu.

A yau Litinin ne dai a ka gudanar da Tanko, tare da sauran mutum biyu da ake zargin sun aikata lefin tare, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotu mai lamba 5 da ke zamanta a Sakateriyar Audu Baƙo.

A zaman na yau, lauyan gwamnati, M. A. Lawan, ya nemi kotu da tambayi waɗanda a ke ƙara na 1, 2 da na 3 ko su na da lauya ko kuma su na son gwamnati ta daukar musu lauya.

Da kotun ta fara tambayar Tanko, wanda shi ne babban wanda a ke zargi da aikata laifin, sai ya ce ba shi da yadda zai yi ya ɗauki lauya, amma ya na son gwamnati ta ɗaukar masa.

Su ma Isyaku da Fatima duk irin tambayar da a ka yi musu kenan, kuma su ka bada amsa iri ɗaya, cewa gwamnati ta ɗaukar musu lauya.

Da ga nan ne sai alƙalin kotun, Mai Shari’a Usman Na-abba, ya baiwa gwamnati umarnin ɗaukar lauya ɗin.

Da ga bisani sai Lawal, wanda shine Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, ya roƙi kotu da ta ɗage sake zama sai ranar 14 ga watan Febrairu domin baiwa gwamnati damar ɗaukar lauyoyin ga wadanda a ke zargi da laifin.

Da ga nan sai Na-abba ya ɗage zaman zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Febrairu.