Home Siyasa Siyasar Nijeriya a lalace ta ke, inji Hafiz Abubakar

Siyasar Nijeriya a lalace ta ke, inji Hafiz Abubakar

0
Siyasar Nijeriya a lalace ta ke, inji Hafiz Abubakar

 

 

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya ce siyasar Nijeriya ta ƙazance ta kuma taɓarɓare.

Abubakar ya baiyana hakan ne a wajen taron wayar da kan matasa a kan harkar mulki karo na 17, wanda Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hula na Arewa, CNG, ta shirya a Jami’ar Bayero Kano, a yau Asabar.

A cewar sa, gyaran wannan kazamin yanayin na siyasar Nijeriya sai an faro ta kan matasa, waɗanda su je shugabannin gobe.

Abubakar ya ƙara da cewa dole ne a sanyawa matasa kishin ƙasa da kuma halaye masu kyau yadda idan sun hau mulki za su canja yanayin siyasa a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa kowa a ƙasar nan, tsofaffi da matasa, sun san cewa yanayin siyasar ƙasar nan ya kazance, inda ya ce “su ma matasan sun san haka kuma suna son a kawo gyara.”

Ya ce irin waɗannan tarurruka na wayar da kan matasa za su yi amfani sosai wajen canja tunanin ƴan ƙasa na siyasar kuɗi, inda ya ƙara da cewa ana kan guguwar hanya a safiyar Nijeriya kuma ya kamata a zabura a kawo gyara mai ɗorewa.

A nashi jawabin, Shugaban Sashen Ilimi na CNG, Jamilu Aliyu, ya jaddada kawo gyara a kan siyasar kuɗi da kuma rashin nagarta a ƙasar nan.

A cewar sa, an radawa taron sunan marigayi Maitama Sule sabo da shi mutum ne mai nagarta.

Ya ce hakan ne ya sanya a ke haɗa taron a lokaci zuwa lokaci domin wayar da kan matasa kan su shiga harkar siyasa a dama da su sannan kuma su zama masu nagarta domin kawo gyara a ƙasar nan