Home Labarai Tauye hakkin bil’adama ne yadda ‘yan sanda suka wulakanta Dino – Falana

Tauye hakkin bil’adama ne yadda ‘yan sanda suka wulakanta Dino – Falana

0
Tauye hakkin bil’adama ne yadda ‘yan sanda suka wulakanta Dino – Falana

Daga Hassan Y.A. Malik

Lauyan nan mai rajin kare hakkin bil adam, Femi Falana mai matsayin SAN, a jiya Alhamis ya caccaki ‘yan sandan Nijeriya bisa yadda suka tafiyar da sake kama Sanata Dino Meleye tare da kai shi gaban kotu daga Abuja har zuwa garin Lokaja a kan gadon asibiti.

Falana ya bayyana yanayin yadda ‘yan sandan suka gudanar da kame da kuma gurfanar da Dino a gaban kotu a matsayin cin zarafi da kuma take hakkin bil adama a bayyane.

Ya ce, “Kama Sanata Dino Melaye alhali yana kan gadon asibiti da ‘yan sanda suka yi a ranar Laraba a Abuja, tare da gurfanar da shi a gaban kotu a Lokoja a ranar Alhamis bai dace ba sam musamman a al’ummar da ke da cikakkiyar doka da oda.

“Wannan abu da ‘yan sanda suka yi ga Dino ba komai bane face cin mutunci da cin zarafinsa da keta alfarmarsa tare da take hakkinsa a matsayinsa na bil adama kamar dai yadda sashe na 34 na kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar da kuma sashe na 7 na kundin tafikar da manyan laifuka na shekarar 2015 ya tanada.”

Falana ya ci gaba da cewa, yadda ‘yan sanda suka yi ga Sanata Dino ya nuna karara yadda gama-garin dan Nijeriya ke shan bakar azaba a hannun jami’an tsaron kasar nan a kowace.

A saboda haka, Falana ya yi kira da majalisar wakilan Nijeriya da ta yi amfani da damarta wajen ganin ta daidaita sahun dukkan wadanda ke da hannu a cin zarafin da aka yi wa Melaye.