
Hukumar Kwana-kwana ta Taraiya, FFS ta ce hayaƙin da a ka gani ya tirniƙe sama da ga ginin Ma’aikatar Kuɗi ta Taraiya da ke Abuja, ya faru ne sakamakon fashewar baturan wutar sola.
Kakakin hukumar FFS, Paul Abraham ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN.
Ya ce a gurin ƴan Kwana-kwana, za a iya samun hayaƙi ba tare da wuta ba, amma ga al’ummar gari, to ko wanne hayaƙi gobara ce.
A cewar Abraham, hukumar ta samu kira ne da misalin ƙarfe 7 na safe cewa gobara ta tashi a Ma’aikatar Kuɗi, inda ya ce tuni a ka tashi jami’ai su ka garzaya wajen domin kashe wutar.
Kakakin ya ƙara da cewa tuni jami’an Kwana-kwanan su ka shawo kan lamarin bangare ma da kwai cikas a harkar hada-hadar al’umma ba.
Haka shi ma Kakakin Ma’aikatar Kuɗi ta Ƙasa, Olajide Oshundun ya tabbatar da cewa batirin sola ne ya janyo wutar.