Home Siyasa Rabon mu da samun ɗan takarar gwamna tun 1992, al’ummar Kano ta Kudu sun koka

Rabon mu da samun ɗan takarar gwamna tun 1992, al’ummar Kano ta Kudu sun koka

0
Rabon mu da samun ɗan takarar gwamna tun 1992, al’ummar Kano ta Kudu sun koka

 

 

 

Ƴan Kano ta Kudu, a ƙarƙashin inuwar Muryar Al’ummar Kano ta Kudu, KSCCF, sun koka cewa tun 1992 rabon da su samu damar mulkin Jihar Kano.

KSCCF ta yi wannan koke ne a wani taron manema labarai a ranar Lahadi, inda Musa Salihu, a madadin Shugaban ƙungiyar, Sanata Masud Eljibrin Doguwa, ya karanta sanarwar Bayan taro.

A cewar kungiyar, Kano ta Kudu, wacce ta ke da Ƙananan Hukumomi mafi yawa a Kano, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a ce ɓangaren ya samu kujerar gwamnan Kano.

A cewar Musa, tun 1992, Kano ta Tsakiya da Kano ta Arewa ne ke yin gwamna, inda ya ƙara da cewa a 2023 ma, Kano ta Kudu ce ya kamata ta fitar da ɗan takarar gwamna amma sai kujerar ta tafi ga Kano ta Tsakiya.

Salihu ya ƙara da cewa Kano ta Kudu na da muhimmiyar rawa da za ta taka a siyasa da ci gaban Kano.

Ya kuma sanar da cewa su al’ummar Kano ta Kudu, su na goyon bayan ɗan majalisar wakilai, Alhassan Rurum a matsayin ɗan takarar gwamna.

Salihu ya ƙara da cewa, KSCCF na goyon bayan Kawu Sumaila a matsayin ɗan takarar Sanata na Kano ta Kudu.