
Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi, ya baiyana cewa Kamfanin Dangote ya bada gudunmawa gagarumar wajen inganta tsaro a Nijeriya, la’akari da yadda ya ke zuba jari mai yawa da kuma samar da ayyukan yi a ƙasar.
Magashi ya baiyana hakan ne a jiya Alhamis a lokacin da ya ziyarci rumfar Dangote a wajen bikin baje kolin ƙasa da ƙasa, karo na 43 a Jihar Kaduna.
Ministan, wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Manjo Janar Ahmed Tijani Jibrin (Rtd) ya ce kamfanin ya yi tasiri sosai wajen inganta tsaro ta hanyar samar da ayyukan yi a kasar nan, kamar yadda sanarwar da ga sashin yaɗa labarai na kamfanin ta baiyana.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa bayan gwamnatin taraiya Dangote ne na biyu wajen Samar da aikin yi a Nigeria.
Dangote ne babban wanda ke daukar nauyin baje kolin kasuwanci na Kaduna da ake yi.
A cewar Magashi, bincike ya nuna akwai alaka tsakanin yanayin tattalin arziki da tsaro, inda ya ce rukunin Kamfanonin Dangote ba wai samar da ayyukan yi kadai yake yi ba, har da tallafawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
Sanarwar ta ce mahalarta taron da ke neman yin kasuwanci da duk wani reshen kamfanin na iya cin gajiyar irin wannan damar a rumfar Kamfanin.
Ta bayyana jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin manyan kasuwanninta a kasar nan, idan aka yi la’akari da matsayinta na tarihi a matsayin hedkwatar siyasar Arewacin Najeriya.