Home Labarai Ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin Azumi — Zulum

Ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin Azumi — Zulum

0
Ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin Azumi — Zulum

 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi alƙawalin cewa ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin fara azumin watan Ramadan.

BBC Hausa ta rawaito cewa Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ziyarar gani-da-ido da tantance ayyukan jin-ƙai da ya kai karo na huɗu a garin Malam-Fatori a ranar Lahadi, kamar yadda sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ta bayyana.

“Iyalai 500 insha Allahu za su isa kafin azumin Ramadan, wannan ne lokacin da ya dace a mayar da su gidajensu na asali cikin aminci da mutunci kafin damina.” In ji Zulum.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya bayyana cewa za a tallafa wa kowanne daga cikin wadanda aka dawo da su da kuɗi naira 100,000 a wani ɓangare na shirin sake raya al’umma.

Sanarwar ta ce za a sake tsukunar da mutanen da suka yi gudun hijira kuma suke zaune a garuruwan Bosso da Diffa da ke kan iyaka da Nijar tun 2014 da suka tsere wa hare-hare a ƙananan hukumomi 10 na arewacin Borno, a matsuguni na wuccin gadi.