Home Labarai Tinubu ya gana da gwamnan Ebonyi, Umahi

Tinubu ya gana da gwamnan Ebonyi, Umahi

0
Tinubu ya gana da gwamnan Ebonyi, Umahi

 

 

 

Jagoran Jami’yar APC na ƙasa a ranar Juma’a ya gana da gwamna David Umahi na jihar Ebonyi.

In za a iya tuna cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori Umahi tare da mataimakinsa a ranar Laraba saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sai dai Umahi ya daukaka kara kan hukuncin.

An jiyo cewa dan takaitaccen ganawar da gwamnan ya yi da Tinubu wanda ya gudana a Abuja ranar Juma’a bazai rasa nasaba da hukuncin kotu ba da kuma rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC.

Tinubu da Umahi dai sun nuna matukar sha’awarsu ta neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a 2023.