
Sanata Adelere Oriolowo da ke wakiltar mazaɓar Osun ta yamma a Majalisar Dattijai ya baiyana cewa batun takarar Mataimakin Ƙasa, Yemi Osinbajo duk jita-jita ne.
Ya ce a siyasar Kudu-maso-Yamma ba wani ɗan takara da a ka sani sai jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a Abuja a jiya Juma’a, Oriolowo ya ce Tinubu lafiya lau ya ke, inda ya “ko a jiki da ƙwaƙwalwa ma an san cewa Tinubu zai iya riƙe ƙasar nan”.
Sanatan ya ƙara da cewa ba ma maganar lafiya ba, Tinubu na da basira da tunanin da zai iya kai ƙasar nan ga gaci.
Ya kuma cewa duk wani ƙuduri na inyamurai na su fitar da ɗan takara ba zai tasyar da Tinubu a kan nashi ƙudurin na tsaya wa ba.