Home Kasuwanci Masu masana’antu na neman ɗaukin gwamnati yayin da farashin man dizel ya kai N720

Masu masana’antu na neman ɗaukin gwamnati yayin da farashin man dizel ya kai N720

0
Masu masana’antu na neman ɗaukin gwamnati yayin da farashin man dizel ya kai N720

 

Ƙungiyar masu Masana’antu ta Ƙasa, MAN na neman tallafin gwamnati na gaggawa a kan samar da kayayyakin, bayan da farashin man dizel ya tashi zuwa N720 a duk lita ɗaya.

Shugaban MAN, reshen jihohin Oyo, Osun, Ekiti da Ondo, Lanre Popoola ne ya yi wannan koken a Ibadan a yau Lahadi yayin da ya ke magana a kan hauhawar farashin man fetur da danginsa da kuma rashin wutar lantarki.

“abu ne mai wuya a riƙa yin aiki a masana’antu a wannan yanayin bayan da farashin man dizel ya tashi zuwa N720 zuwa N730 a duk lita.

“Ai da matuƙar wahala a riƙa samar da kayaiyaki a wannan yanayi duba da cewa kashi 70 na masana’antu da man dizel su ke amfani. Ban san ya za mu yi ba.

“Gashi ba wuta. Wutar da munke samu yanzu ba ta fi kashi talatin ɗin ta da ba. Ga kuɗaɗen da mutane su ke samu ba ƙaruwa ya ke ba. Ga farashin kayaiyaki sai tashin gwauron zabi ya ke yi.

“ko a masana’anta ta yanzu mun rage awannin yin aiki. Da karɓa-karɓar aiki uku munke yi a rana na awa takwas-takwas, yanzu kuwa karɓa ɗaya kawai munke iya yi,” in ji shi.