
A yau Litinin ne Babbar Kotun Taraiya da ke Abuja ta sanya ranar 28 a matsayin ranar da za ta yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a kan belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda, Abba Kyari.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya sanya ranar bayan ya saurari muhawara tsakanin lauyan mai ƙara da wanda a ke ƙara.
Lauyan NDLEA, Sunday Joseph ya shaidawa kotun cewa wanda a ke ƙara na 4 da na 5 ba su bada haɗin kai ba, inda ya roƙi kotun da ta basu umarnin rubuta takardar rantsuwar yin da’a.
Daga nan ne sai kotun ta bada umarnin a mayar da Abba Kyari da sauran waɗanda a ke zargi tare da shi zuwa gidan yarin har sai 28 ga Maris domin yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a kan belin na sa.