Home Labarai Ƴan gudun hijira sun koka kan zargin karkatar da katin biyan kuɗin abinci na wata-wata

Ƴan gudun hijira sun koka kan zargin karkatar da katin biyan kuɗin abinci na wata-wata

0
Ƴan gudun hijira sun koka kan zargin karkatar da katin biyan kuɗin abinci na wata-wata

 

Wasu ƴan gudun hijira a sansanin Gubio a Maiduguri sun yi zargin cewa a na karkatar da katin biyan su kuɗin abinci na wata-wata.

Shi katin, wani ɓangare ne na Shirin Abinci na Duniya, WFP da a ke baiwa ƴan gudun hijira su riƙa cirar kuɗi na sayen abinci a ƙarshen wata.

A duk ƙarshen wata ne a ke saka kuɗin sai ƴan gudun hijirar su je su xora ta katin.

Wasu da ga cikin yan gudun hijiran da su ka tattauna da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN sun yi kira ga gwamnati da WFP da a binciki jami’an da ke harkar rabon kuɗaɗen domin a gano wadanda su ke karkatar da haƙƙin nasu.

Sun ce an saba basu kuɗaɗen a hannu, amma da a ka ƙirkiro da biyan kuɗin ta kati, yanzu watanni biyu kenan ba a basu ba duk da an sa sun buɗe asusun banki.

Sun ƙara da cewa an rarraba wa wasu lambobin sirri domin amfani da su wajen cire kuɗaɗen.

Wasu kuma sun shaida wa NAN cewa sama da watanni shida ba su samu kuɗaɗen nasu ba.

Wani jami’in Hukumar Jin ƙari ta Jihar Borno, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce sun samu ƙorafin kuma tuni a ka fara bincike a kan hakan.