
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya baiyana cewa Jagoran APC na Ƙasa, Bola Tinubu ya taɓa cewa zai yi masa Mataimaki lokacin da shi Atikun ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyar ACN.
Atiku ya baiyana hakan ne yayin tattaunawa da Kwamitin Amintattu na PDP a Abuja.
A cewar Atiku, bai yarda ya baiwa Tinubu mataimakin ba sabo da ya na son ya ɗauko wanda zai masa Mataimaki da ga Kudu-maso-Gabas, inda ya dauko Sanata Ben Obi.
Atiku ya ƙara da cewa wasu su na cewa ba a baiwa Kudu-maso-Gabas dama, gashi kuma ya ƙi yarda da roƙon Tinubu, duk da shi ya bashi (Atiku) tikitin takarar ya kuma sanya masa sharuɗɗa, amma bai yarda ba, ya je ya dauko da ga ɓangaren na inyamirai.
“Sai na cewa Tinubu, ba zan dauke ka ba, shi ne na dauko Ben Obi,” in ji Atiku.
Atiku ya kuma tuna sanda ya ƙara ɗaukar Mataimaki da ga Kudu-maso-Gabas, inda ya dauki Peter Obi a 2019, lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyar PDP.
Daga nan ne sai Atiku ya ce bai ga dalilin da ƴan Kudu-maso-Gabas za su ce ba a basu dama ba, musamman duba da tarihin da ya bayar.